Zefaniya 2:4-7
4
Za a yashe Gaza a kuma bar Ashkelon kango. Da tsakar rana Ashdod za tă zama babu kowa a kuma tumɓuke Ekron.
5
Taku ta ƙare ku da kuke zama a bakin teku, Ya ku mutanen Keretawa; maganar Ubangiji tana gāba da ke, Ya ke Kan’ana, ƙasar Filistiyawa. “Zan hallaka ki kuma babu abin da zai rage.”
6
Ƙasar da take a bakin teku, inda Keretawa suke zaune, za tă zama wurin da makiyaya da ta garken tumaki.
7
Za tă zama mallakar raguwar gidan Yahuda; a can za su sami wurin kiwo. Da yamma za su kwanta a gidajen Ashkelon. Ubangiji Allahnsu zai lura da su; zai maido musu da martabarsu.
Settings