Zefaniya 2:8-11
8
“Na ji irin zagin da Mowab take yi, da kuma ba’ar Ammonawa, waɗanda suka zagi mutanena suna kuma yi barazana a kan ƙasarsu.
9
Saboda haka, muddin ina raye,” in ji Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, “tabbatacce Mowab za tă zama kamar Sodom, Ammonawa kuma kamar Gomorra, ƙasa mai ciyayi da rammukan gishiri, ƙasa marar amfani har abada. Raguwar mutanena za su washe su; waɗanda suka rage na al’ummata za su gāda ƙasarsu.”
10
Wannan ne zai zama sakamakon girmankansu, saboda zagi da kuma ba’ar da suka yi wa mutanen Ubangiji Maɗaukaki.
11
Ubangiji zai zama abin tsoro a gare su sa’ad da ya hallaka allolin ƙasar. Al’ummai a kowane bakin teku za su yi masa sujada, kowa a ƙasarsa.
Settings