Zakariya 14:1-9
1
Ranar Ubangiji tana zuwa sa’ad da za a raba muku ganimar da aka washe daga gare ku.
2
Zan tara dukan al’ummai su yaƙi Urushalima; za a ci birnin da yaƙi, za a washe gidaje, a kuma yi wa mata fyaɗe. Rabin birnin zai je bauta, amma ba za a kwashe sauran mutanen daga birnin ba.
3
Sa’an nan Ubangiji zai fita yă yi yaƙi da waɗannan al’ummai, kamar yadda yake yaƙi a ranar yaƙi.
4
A ranan nan ƙafafunsa za su tsaya a kan Dutsen Zaitun, gabas da Urushalima, za a kuma tsage Dutsen Zaitun kashi biyu daga gabas zuwa yamma, yă zama babban kwari, rabin dutsen zai matsa zuwa wajen arewa, rabi kuma zai matsa zuwa wajen kudu.
5
Za ku gudu ta wajen kwarin dutsena, gama zai miƙe har zuwa Azel. Za ku gudu kamar yadda kuka guje wa girgizar ƙasa a kwanakin Uzziya sarkin Yahuda. Sa’an nan Ubangiji Allahna zai zo, tare da duk masu tsarki.
6
A ranan nan ba za a kasance da haske ko sanyi ba, ko hazo mai duhu ba.
7
Za tă zama rana ce ta musamman, ba yini ko dare, rana da take sananne ga Ubangiji. Sa’ad da yamma ta yi, za a yi haske.
8
A ranan nan ruwan rai zai kwararo daga Urushalima, rabi zai gangara gabas zuwa teku rabi kuma zai gangara yamma zuwa Bahar Rum, a damina da rani.
9
Ubangiji zai sama sarki bisa dukan duniya. A ranan nan za a kasance da Ubangiji ɗaya, ba wani suna kuma sai nasa.
Settings