Zakariya 11:8
Ana nuna aya 8 tare da mahallin da ke kewaye.
5
Masu sayensu sun yanyanka su, suka kuwa tafi ba hukunci. Masu sayar da su sun ce, ‘Yabi Ubangiji, na yi arziki!’ Makiyayansu ma ba su ji tausayinsu ba.
6
Gama ba zan ƙara jin tausayin mutanen ƙasar ba,” in ji Ubangiji. “Zan ba da kowa ga maƙwabcinsa da kuma sarkinsa. Za su zalunci ƙasar, ba zan kuma cece su daga hannuwansu ba.”
7
Saboda haka na yi kiwon garken da za a yanka, musamman garken da ake zalunta. Sai na ɗauki sanduna biyu na kira ɗaya Tagomashi, ɗaya kuma Haɗinkai, sai na yi kiwon garken.
8
Cikin wata guda na kawar da makiyayan nan uku. Garken suka ƙi ni, na kuwa gaji da su
9
na ce, “Ba zan zama makiyayinku ba. Bari masu mutuwa su mutu, masu hallaka kuma su hallaka. Bari waɗanda suka ragu su ci naman juna.”
10
Sai na ɗauki sandana mai suna Tagomashi na karya shi, na janye alkawarin da na yi da dukan al’ummai.
11
An janye shi a ranan nan, saboda haka garken da yake cikin wahala masu kallona sun san cewa maganar Ubangiji ce.
Settings