Skip to content
Waƙar Waƙoƙi 6:4-10

Waƙar Waƙoƙi 6:4-10

4
Ke kyakkyawa ce, ƙaunatacciyata, kamar Tirza, kyakkyawa kuma kamar Urushalima, mai daraja kamar mayaƙa da tutoti.
5
Ki kau da idanu daga gare ni; gama suna rinjayata. Gashinki yana kama da garken awakin da suke gangarawa daga Gileyad.
6
Haƙoranki suna kama da garken tumakin da suke haurawa daga inda aka yi musu wanka. Kowanne yana tare da ɗan’uwansa; babu waninsu da yake shi kaɗai.
7
Kumatunki sun yi kamar rumman da aka tsaga biyu a cikin lulluɓinki.
8
Sarauniyoyi sittin za su iya kasance a can, da ƙwarƙwarai tamanin da kuma budurwai da suka wuce ƙirge;
9
amma kurciyata, cikakkiyata, dabam take, tilo kuwa ga mahaifiyarta, ’yar lele ga wadda ta haife ta. ’Yan mata sun gan ta suka ce da ita mai albarka; sarauniyoyi da ƙwarƙwarai sun yabe ta.
10
Wace ce wannan da ta bayyana sai ka ce ketowar alfijir? Kyakkyawa kamar wata, mai haske kamar rana, mai daraja kamar taurari a jere?
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options