Waƙar Waƙoƙi 4:1-5
1
Ke kyakkyawa ce, ƙaunatacciyata! Kai, ke kyakkyawa ce! Idanunki sun yi kamar na kurciya a cikin lulluɓinki. Gashinki ya yi kamar garken awaki da suke gangarawa daga Dutsen Gileyad.
2
Haƙoranki sun yi kamar garken tumakin da ba a daɗe da yin musu sausaya ba, da suke haurawa daga inda aka yi musu wanka. Kowanne yana tare da ɗan’uwansa; babu waninsu da yake shi kaɗai.
3
Leɓunanki kamar zaren jan garura bakinki yana da kyau. Kumatunki sun yi kamar rumman da aka tsaga biyu a cikin lulluɓinki.
4
Wuyanki ya yi kamar hasumiyar Dawuda, da aka gina da daraja; a kansa an rataye garkuwoyi dubu, dukansu garkuwoyin jarumawa ne.
5
Nonanki biyu sun yi kamar bareyi biyu, kamar tagwayen barewa da suke kiwo a cikin furen bi-rana.
Settings