Skip to content
Waƙar Waƙoƙi 3:6-11

Waƙar Waƙoƙi 3:6-11

6
Wane ne wannan mai zuwa daga hamada kamar tunnuƙewar hayaƙi, cike da ƙanshin turaren mur da lubban da aka yi da kayan yajin ’yan kasuwa?
7
Duba! Abin ɗaukar Solomon ne, jarumawa sittin suke rakiya, zaɓaɓɓun sojojin Isra’ila,
8
dukansu suna saye da takobi dukansu ƙwararru ne a yaƙi, kowanne da takobinsa a rataye a gefensa, a shirye don abubuwan bantsoro na dare.
9
Sarki Solomon ya yi wa kansa abin ɗauka; ya yi shi da katako daga Lebanon.
10
An yi sandunansa da azurfa, aka yi ƙasarsa da zinariya. An lulluɓe wurin zaman da zanen shunayya, ’yan matan Urushalima sun yi mata irin yayen da ake yi na ƙauna.
11
Fito, ku ’yan matan Sihiyona, ku ga Sarki Solomon yana saye da rawani, rawanin da mahaifiyarsa ta naɗa masa, a ranar aurensa, a ranar da zuciyarsa ta yi farin ciki.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options