Waƙar Waƙoƙi 3:11
Ana nuna aya 11 tare da mahallin da ke kewaye.
8
dukansu suna saye da takobi dukansu ƙwararru ne a yaƙi, kowanne da takobinsa a rataye a gefensa, a shirye don abubuwan bantsoro na dare.
9
Sarki Solomon ya yi wa kansa abin ɗauka; ya yi shi da katako daga Lebanon.
10
An yi sandunansa da azurfa, aka yi ƙasarsa da zinariya. An lulluɓe wurin zaman da zanen shunayya, ’yan matan Urushalima sun yi mata irin yayen da ake yi na ƙauna.
11
Fito, ku ’yan matan Sihiyona, ku ga Sarki Solomon yana saye da rawani, rawanin da mahaifiyarsa ta naɗa masa, a ranar aurensa, a ranar da zuciyarsa ta yi farin ciki.
Settings