Romawa 7:1-11
1
Ba ku sani ba, ’yan’uwa, ina magana ne fa da mutanen da suka san doka, cewa dokar tana da iko a kan mutum muddin yana a raye ne kawai.
2
Misali, bisa ga doka mace mai aure tana daure ga mijinta muddin mijin yana da rai, amma in mijinta ya mutu, an sake ta ke nan daga dokar aure.
3
Saboda haka fa, in ta auri wani yayinda mijinta yana raye, za a ce da ita mazinaciya. Amma in mijinta ya mutu, an sake ta ke nan daga wannan doka, ita kuwa ba mazinaciya ba ce, ko da yake ta auri wani.
4
Saboda haka ’yan’uwana, ku ma kun mutu ga dokar ta wurin jikin Kiristi, domin ku zama na wani, gare shi wanda aka tashe shi daga matattu, don mu ba da amfani ga Allah.
5
Gama sa’ad da halin mutuntaka yake mulkinmu, sha’awace-sha’awacen zunubi waɗanda dokar ta zuga sun yi ta aiki a jikunanmu, don mu ba da amfani wa mutuwa.
6
Amma yanzu, ta wurin mutuwa ga abin da dā ya daure mu, an sake mu daga dokar saboda mu yi hidima a sabuwar hanyar Ruhu, ba a tsohuwar hanyar rubutaccen ƙa’ida ba.
7
Me za mu ce ke nan? Dokar zunubi ce? Sam, ko kaɗan! Tabbatacce ai, da ban san mene ne zunubi ba in ba ta wurin doka ba. Gama da ban san mene ne ƙyashi yake ba tabbatacce in ba don doka ta ce, “Kada ka yi ƙyashi ba.”
8
Amma zunubi, da ya sami dama ta wurin umarnin nan, ya haifar a cikina kowane halin ƙyashi iri-iri. Gama in babu doka, zunubi matacce ne.
9
Dā kam ina da rai sa’ad da ban san doka ba; amma da umarni ya zo, sai zunubi ya zaburo da rai na kuma mutu.
10
Na gane cewa wannan umarnin da aka nufa ya kawo rai, a gaskiya ya jawo mutuwa ce.
11
Gama zunubi, da ya sami dama ta wurin umarni, sai ya ruɗe ni, kuma ta wurin umarnin kuwa ya kashe ni.
Settings