Romawa 15:1-7
1
Mu da muke da ƙarfi ya kamata mu yi haƙuri da kāsawar marasa ƙarfi ba kawai mu gamshi kanmu ba.
2
Ya kamata kowannenmu yă faranta wa maƙwabcinsa rai don kyautata zamansa domin kuma yă gina shi.
3
Gama ko Kiristi ma bai gamshi kansa ba, amma kamar yadda yake a rubuce cewa, “Zage-zagen da waɗansu suka yi maka, duk sun fāɗo a kaina.”
4
Gama duk abin da aka rubuta a dā an rubuta ne domin yă koya mana, don ta wurin jimrewa da kuma ƙarfafawar Nassosi mu kasance da bege.
5
Bari Allah mai ba da haƙuri da kuma ƙarfafawa yă ba ku ruhun haɗinkai da juna yayinda kuke bin Kiristi Yesu,
6
don da zuciya ɗaya da kuma baki ɗaya kuke ɗaukaka Allah da kuma Uban Ubangijinmu Yesu Kiristi.
7
Ta haka sai ku karɓi juna kamar yadda Kiristi ya karɓe ku, don a yabi Allah.
Settings