Romawa 15:7-13
7
Ta haka sai ku karɓi juna kamar yadda Kiristi ya karɓe ku, don a yabi Allah.
8
Ina dai gaya muku cewa Kiristi ya zama bawan Yahudawa a madadin gaskiyar Allah, don yă tabbatar da alkawaran da aka yi wa kakannin kakanninmu
9
domin Al’ummai su ɗaukaka Allah saboda jinƙansa, kamar yadda yake a rubuce, “Saboda haka zan yabe ka a cikin Al’ummai; zan rera waƙoƙi ga sunanka.”
10
Ya kuma ce, “Ku yi farin ciki, ya Al’ummai, tare da mutanensa.”
11
Da kuma, “Ku yabi Ubangiji, dukanku Al’ummai, ku kuma rera masa yabo, dukanku mutanen duniya.”
12
Kuma Ishaya ya ce, “Tushen Yesse zai tsiro, wanda zai taso yă yi mulkin al’ummai; al’ummai za su sa bege a gare shi.”
13
Bari Allah na bege yă cika ku da matuƙar farin ciki da salama yayinda kuke dogara gare shi, domin ku yalwata cikin bege ta wurin ikon Ruhu Mai Tsarki.
Settings