Skip to content
Romawa 12:9-21

Romawa 12:9-21

9
Dole ƙauna tă zama ta gaskiya. Ku ƙi duk abin da yake mugu; ku manne wa abin da yake nagari.
10
Ku ba da kanku ga juna cikin ƙauna irin ta ’yan’uwa. Kowa yă yi ƙoƙari wajen girmama wani fiye da kansa.
11
Kada ku zama marasa himma, sai dai masu himma a ruhaniyarku, kuna bauta wa Ubangiji.
12
Ku yi farin ciki cikin bege, haƙuri cikin shan wuya, aminci cikin addu’a.
13
Ku taimaki mutanen Allah masu bukata. Ku zama masu karɓan baƙi.
14
Ku sa wa masu tsananta muku albarka; ku sa albarka kada fa ku la’anta.
15
Ku yi murna da masu murna, ku yi kuka da masu kuka.
16
Ku yi zaman lafiya da juna. Kada ku nuna girman kai, sai ma ku riƙa cuɗanya da talakawa. Kada ku zama masu ɗaga kai.
17
Idan kowa ya yi muku mugunta, kada ku sāka masa da mugunta. Ku lura don ku aikata abin da kowa zai iya gani cewa daidai ne.
18
Ku yi iya ƙoƙarinku, in zai yiwu, ku yi zaman lafiya da kowa.
19
Kada ku yi ramuwa, abokaina, sai dai ku bar wa Allah. Gama a rubuce yake cewa, “Ramuwa tawa ce; zan kuwa sāka,” in ji Ubangiji.
20
A maimakon haka, “In abokin gābanka yana jin yunwa, ka ciyar da shi; in yana jin ƙishirwa, ka ba shi ruwan sha. Ta yin haka, za ka tara garwashin wuta a kansa.”
21
Kada ku bar mugunta ta sha kanku, sai dai ku sha kan mugunta ta wurin aikata nagarta.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options