Ru’uya ta Yohanna 9:13-21
13
Mala’ika na shida ya busa ƙahonsa, sai na ji murya tana fitowa daga ƙahonin bagaden zinariya da suke a gaban Allah.
14
Ta ce wa mala’ika na shida da yake da ƙahon, “Ka saki mala’iku huɗun nan da suke a daure a babban kogin Yuferites.”
15
Mala’iku huɗun nan kuwa da aka shirya musamman don wannan sa’a da kuma don wannan rana da wata da kuma shekara aka sake su domin su kashe kashi ɗaya bisa uku na ’yan Adam.
16
Yawan rundunan masu hawan dawakan nan mutum miliyon ɗari biyu ne. Na ji adadinsu.
17
Dawakai da masu hawansu da na gani cikin wahayina sun yi kamar. Sulkunansu ja wur ne, baƙin shuɗi, da kuma rawaya kamar farar wuta. Kawunan dawakan sun yi kamar kawunan zakoki, daga bakunansu kuwa wuta, hayaƙi, da farar wuta suna fitowa.
18
Aka kashe kashi ɗaya bisa uku na ’yan Adam da annobai uku na wuta, hayaƙi da farar wuta da suka fito daga bakunansu.
19
Ƙarfin dawakan nan kuwa yana a bakunansu da wutsiyoyinsu; gama wutsiyoyinsu suna kama da macizai masu kawuna, da wutsiyoyin ne kuma suke yi wa mutane rauni.
20
Sauran ’yan Adam da ba a kashe ta wajen waɗannan annobai ba kuwa har wa yau ba su tuba daga aikin hannuwansu ba; ba su daina bauta wa aljanu, da gumakan zinariya, azurfa, tagulla, dutse da na itace, gumakan da ba sa iya gani ko ji ko tafiya ba.
21
Ba su kuma tuba daga kisankansu, sihirinsu, fasikancinsu ko kuma daga sace-sacensu ba.
Settings