Ru’uya ta Yohanna 5:5-10
5
Sai ɗaya daga cikin dattawan ya ce mini, “Kada ka yi kuka! Duba, Zakin kabilar Yahuda, da kuma Tushen Dawuda ya ci nasara. Ya iya buɗe naɗaɗɗen littafin da hatimansa bakwai.”
6
Sa’an nan na ga Ɗan Rago, yana kamar an yanka, tsaye a tsakiyar kursiyin, halittu huɗun nan masu rai da kuma dattawan an sun kewaye shi. Yana da ƙahoni bakwai da idanu bakwai, waɗanda suke ruhohi bakwai na Allah da aka aika cikin dukan duniya.
7
Ya zo ya karɓi naɗaɗɗen littafin daga hannun dama na wannan wanda yake zaune a kursiyin.
8
Bayan ya karɓa, sai halittu huɗun nan masu rai da kuma dattawan nan ashirin da huɗu suka fāɗi ƙasa a gaban Ɗan Ragon. Kowannensu yana da garaya kuma suna riƙe da kaskon zinariya cike da turare, waɗanda suke addu’o’in tsarkaka.
9
Suka rera sabuwar waƙa, “Ka cancanci ka karɓi naɗaɗɗen littafin ka kuma buɗe hatimansa, domin an kashe ka, da jininka kuma ka sayi mutane wa Allah, daga kowace kabila da harshe da mutane da kuma al’umma.
10
Ka mai da su masarauta da kuma firistoci, don su yi wa Allahnmu hidima, kuma za su yi mulki a duniya.”
Settings