Zabura 90:3-11
3
Ka komar da mutane zuwa ƙura, kana cewa, “Ku koma ƙura, ya ku ’ya’yan mutane.”
4
Gama shekaru dubu a gabanka kamar kwana ɗaya ne da ya wuce, ko sa’a guda na dare.
5
Ka share mutane cikin barcin mutuwa; suna kama da sabuwa ciyawar safiya,
6
ko da yake da safe takan yi sabuwar huda da yamma sai ta bushe ta kuma yanƙwane.
7
An cinye mu ta wurin fushinka mun kuma razana ta wurin hasalarka.
8
Ka ajiye laifinmu a gabanka, asirin zunubanmu a hasken kasancewarka.
9
Dukan kwanakinmu sun wuce ƙarƙashin fushinka; mun gama shekarunmu da nishi.
10
Tsawon kwanakinmu shekaru saba’in ne, ko tamanin, in muna da ƙarfi; duk da haka tsawonsu wahaloli ne kawai da ɓacin rai, gama da sauri suke wucewa, ta mu kuma ta ƙare.
11
Wa ya san ƙarfin fushinka? Gama hasalarka tana da girma kamar tsoron da ya dace da kai.
Settings