Zabura 90:1-6
1
Addu’ar Musa Mutumin Allah. Ubangiji kai ne mazauninmu cikin dukan zamanai.
2
Kafin a haifi duwatsu ko a fid da ƙasa da duniya, daga madawwami zuwa madawwami kai Allah ne.
3
Ka komar da mutane zuwa ƙura, kana cewa, “Ku koma ƙura, ya ku ’ya’yan mutane.”
4
Gama shekaru dubu a gabanka kamar kwana ɗaya ne da ya wuce, ko sa’a guda na dare.
5
Ka share mutane cikin barcin mutuwa; suna kama da sabuwa ciyawar safiya,
6
ko da yake da safe takan yi sabuwar huda da yamma sai ta bushe ta kuma yanƙwane.
Settings