Zabura 86:1-7
1
Addu’ar Dawuda. Ka ji, ya Ubangiji, ka kuma amsa mini, gama ni matalauci ne mai bukata kuma.
2
Ka tsare raina, gama na ba da kaina gare ka. Kai ne Allahna; ka ceci bawanka wanda ya dogara gare ka.
3
Ka yi mini jinƙai, ya Ubangiji, gama na yi kira gare ka dukan yini.
4
Ka ba bawanka farin ciki gama gare ka, ya Ubangiji, na miƙa raina.
5
Kai mai gafartawa da kuma mai alheri ne, ya Ubangiji, cike da ƙauna ga dukan waɗanda suke kira gare ka.
6
Ka ji addu’ata, ya Ubangiji; ka saurari kukata na neman jinƙai.
7
A lokacin wahala zan yi kira gare ka, gama za ka amsa mini.
Settings