Skip to content
Zabura 69:29-36

Zabura 69:29-36

29
Ina cikin zafi da kuma azaba; bari cetonka, ya Allah, yă tsare ni.
30
Zan yabe sunan Allah cikin waƙa in kuma ɗaukaka shi tare wurin yin godiya.
31
Wannan zai gamshi Ubangiji fiye da saniya, fiye da bijimi da ƙahoninsa da kuma kofatansa.
32
Matalauta za su gani su kuma yi murna, ku da kuke neman Allah, bari zukatanku su rayu!
33
Ubangiji yakan ji masu bukata ba ya kuwa ƙyale kamammun mutanensa.
34
Bari sama da ƙasa su yabe shi, tekuna da dukan abin da yake motsi a cikinsu,
35
gama Allah zai cece Sihiyona yă sāke gina biranen Yahuda. Sa’an nan mutane za su zauna a can su mallake ta,
36
’ya’yan bayinsa za su gāje ta, waɗanda kuma suna ƙaunar sunansa za su zauna a can.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options