Skip to content
Zabura 69:22-29

Zabura 69:22-29

22
Bari teburin da aka shirya a gabansu yă zama musu tarko; bari yă zama sakamakon laifi da kuma tarko.
23
Bari idanunsu yă dushe don kada su gani, bayansu kuma yă tanƙware har abada.
24
Ka kwarara fushinka a kansu; bari fushinka mai zafi yă ci musu.
25
Bari wurinsu yă zama kufai; kada ka bar wani yă zauna a tentunansu.
26
Gama sun tsananta wa waɗanda ka hukunta suna kuma taɗin wahalar waɗanda ka ji musu rauni.
27
Ka neme su da laifi a kan laifi; kada ka bar su su sami rabo a cikin cetonka.
28
Bari a shafe su sarai daga littafin rai kada a kuma lissafta su tare da adalai.
29
Ina cikin zafi da kuma azaba; bari cetonka, ya Allah, yă tsare ni.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options