Zabura 6:1-7
1
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da kayan kiɗi masu tsirkiya. Bisa ga sheminit. Ta Dawuda. Ya Ubangiji, kada ka tsawata mini cikin fushinka ko ka hore ni cikin hasalarka.
2
Ka yi mini jinƙai, Ubangiji, gama na suma; Ya Ubangiji, ka warkar da ni, gama ƙasusuwana suna zafin ciwo.
3
Raina yana cikin wahala. Har yaushe, ya Ubangiji, har yaushe?
4
Ka juyo, ya Ubangiji, ka cece ni; ka cece ni saboda madawwamiyar ƙaunarka.
5
Babu wanda yakan tuna da kai sa’ad da ya mutu. Wa ke yabonka daga kabari?
6
Na gaji tiƙis daga nishi. Dukan dare na jiƙe gadona da kuka na jiƙe kujerata da hawaye.
7
Idanuna sun rasa ƙarfi da baƙin ciki; sun rasa ƙarfi saboda dukan abokan gābana.
Settings