Zabura 50:16-22
16
Amma ga mugaye, Allah ya ce, “Wace dama ce kuke da ita na haddace dokokina ko na yin maganar alkawarina a leɓunanku?
17
Kun ƙi umarnina kuka kuma zubar da kalmomina a bayanku
18
Sa’ad da kuka ga ɓarawo, kukan haɗa kai da shi; kukan haɗa kai da mazinata.
19
Kuna amfani da bakunanku don mugunta kuna kuma gyara harshenku don ruɗu.
20
Kuna ci gaba da magana a kan ɗan’uwanku ku kuma yi maganar ƙarya a kan ɗan mahaifinku.
21
Kun yi waɗannan abubuwa na kuwa yi shiru; kun ɗauka gaba ɗaya ni kamar ku ne. Amma zan tsawata muku in kuma zarge ku a fuskarku.
22
“Ku lura da wannan, ku da kuka manta da Allah, ko kuwa in yayyage ku kucu-kucu, ba kuma wanda zai cece ku.
Settings