Zabura 50:16-21
16
Amma ga mugaye, Allah ya ce, “Wace dama ce kuke da ita na haddace dokokina ko na yin maganar alkawarina a leɓunanku?
17
Kun ƙi umarnina kuka kuma zubar da kalmomina a bayanku
18
Sa’ad da kuka ga ɓarawo, kukan haɗa kai da shi; kukan haɗa kai da mazinata.
19
Kuna amfani da bakunanku don mugunta kuna kuma gyara harshenku don ruɗu.
20
Kuna ci gaba da magana a kan ɗan’uwanku ku kuma yi maganar ƙarya a kan ɗan mahaifinku.
21
Kun yi waɗannan abubuwa na kuwa yi shiru; kun ɗauka gaba ɗaya ni kamar ku ne. Amma zan tsawata muku in kuma zarge ku a fuskarku.
Settings