Skip to content
Zabura 49:11-20

Zabura 49:11-20

11
Kaburburansu za su ci gaba da zama gidajensu har abada, Can za su kasance har zamanai marasa ƙarewa, ko da yake sun ba wa filaye sunayen kansu.
12
Amma mutum, kome arzikinsa, ba ya dawwama; shi kamar dabbobi ne da suke mutuwa.
13
Wannan ne ƙaddarar waɗanda suke dogara a kansu, da kuma ta mabiyansu, waɗanda suka tabbatar da faɗinsu. Sela
14
Kamar tumaki an ƙaddara su ga kabari; za su kuwa zama abincin mutuwa amma masu gaskiya za su yi mulki a kansu da safe. Kamanninsu za su ruɓe a cikin kabari, nesa da gidajensu masu tsada.
15
Amma Allah zai ceci raina daga kabari; tabbatacce zai ɗauke ni zuwa wurinsa. Sela
16
Kada ka razana da yawa sa’ad da mutum ya yi arziki sa’ad da darajar gidansa ta ƙaru;
17
gama ba zai ɗauki kome tare da shi sa’ad da ya mutu ba, darajarsa ba za tă gangara tare da shi ba.
18
Ko da yake yayinda yake a raye ya ɗauka kansa mai albarka ne, mutane kuma sun yabe ka sa’ad da kake cin nasara,
19
zai gamu da tsarar kakanninsa, waɗanda ba za su taɓa ganin hasken rayuwa ba.
20
Mutumin da yake da arziki ba tare da ganewa ba shi kamar dabbobi ne da suke mutuwa.
Settings

Reading style

Typeface

Font size 19px

Reading width 75 chars

Options