Zabura 21:1-7
1
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Zabura ta Dawuda. Ya Ubangiji, sarki yana farin ciki cikin ƙarfinka. Yana farin cikinsa ƙwarai cikin nasarorin da ka ba shi!
2
Ka biya masa bukatar zuciyarsa ba ka kuwa hana masa roƙon da ya yi da leɓunansa ba. Sela
3
Ka marabce shi da yalwar albarka ka kuma sa masa rawanin zallan zinariya a kansa.
4
Ya nemi ka ba shi rai, ka kuwa ba shi, tsawo kwanaki, har abada abadin
5
Ta wurin nasarorin da ka ba shi, ɗaukakarsa mai girma ce; ka mayar masa ɗaukaka da kuma suna.
6
Tabbatacce ka ba shi madawwamiyar albarka ka kuma sa shi murna da farin cikin kasancewarka.
7
Gama sarki ya dogara gare ka Ubangiji ta wurin ƙauna marar ƙarewa ta Mafi Ɗaukaka ba zai jijjigu ba.
Settings