Zabura 18:6-16
6
Cikin wahalata na yi kira ga Ubangiji; Na yi kuka ga Allahna don taimako. A Haikalinsa ya ji muryata, Kukana na neman taimako ya kai kunnensa.
7
Ƙasa ta yi rawa ta kuma girgiza, tussan duwatsu sun girgiza; sun yi rawa domin ya yi fushi.
8
Hayaƙi ya tashi daga kafan hancinsa; wuta mai ci daga bakinsa, garwashi wuta mai ci daga bakinsa.
9
Ya buɗe sammai ya sauko; baƙaƙen gizagizai suna a ƙarƙashin ƙafafunsa.
10
Ya hau kerubobi ya kuma yi firiya; ya yi shawagi a fikafikan iska.
11
Ya mai da duhu abin rufuwarsa, rumfa kewaye da shi, baƙaƙen gizagizan ruwan sama na sarari,
12
daga cikin hasken kasancewarsa gizagizai suka yi gaba, da ƙanƙara da kuma walƙiya.
13
Ubangiji ya yi tsawa daga sama; muryar Mafi Ɗaukaka ya yi kāra.
14
Ya harba kibiyoyinsa ya kuma watsar da abokan gāba, walƙiya mai girma ya fafare su.
15
Kwarin teku sun bayyana tussan duniya sun bayyana a fili sa’ad da ka tsawata, ya Ubangiji, sa’ad da ka numfasa daga hancinka.
16
Ya miƙa hannunsa daga sama ya kama ni; ya ja ni daga zurfin ruwaye.
Settings