Zabura 141:1-4
1
Zabura ta Dawuda. Na yi kira gare ka, ya Ubangiji; ka zo da sauri. Ka ji muryata sa’ad da na yi kira.
2
Bari a sa addu’ata a gabanka kamar turaren ƙonawa; bari ɗagawa hannuwana ta zama kamar hadayar yamma.
3
Ka sa mai tsaro a bakina, ya Ubangiji; ka yi tsaron ƙofar leɓunana.
4
Kada ka bar zuciyata ta juya ga yin abin da yake mugu, ta sa kai ga aikata mugayen ayyuka tare da mutane masu aikata mugunta; kada ka bari in ci abincinsu.
Settings