1
Waƙar haurawa. Na tā da idanuna gare ka, gare ka da kursiyinka yake cikin sama.
2
Kamar yadda idanun bayi suna duban hannun maigidansu, kamar yadda idanun baiwa suna duban hannun uwargijiyarta, haka idanunmu suna duban Ubangiji Allahnmu, sai ya nuna mana jinƙansa.