Zabura 119:81-88
81
Raina ya tafke da marmari don cetonka, amma na sa zuciyata a maganarka.
82
Idanuna sun gaji, suna jiran alkawarinka; Na ce, “Yaushe za ka ta’azantar da ni?”
83
Ko da yake ni kamar salkar ruwan inabi ne a cikin hayaƙi, ban manta da ƙa’idodinka ba.
84
Har yaushe bawanka zai yi ta jira? Yaushe za ka hukunta masu tsananta mini?
85
Masu girman kai sun haƙa mini rami, sun ƙetare dokarka.
86
Dukan umarnanka abin dogara ne; ka taimake ni, gama mutane suna tsananta mini ba dalili.
87
Sun kusa gama da ni a duniya, amma ban bar bin farillanka ba.
88
Ka kiyaye raina bisa ga ƙaunarka, zan kuwa yi biyayya da farillan bakinka.
Settings