Zabura 119:73-80
73
Hannuwanka ne suka yi suka kuma siffanta ni; ka ba ni ganewa don in koyi umarnanka.
74
Bari waɗanda suke tsoronka su yi farin ciki sa’ad da suke gan ni, gama na sa zuciyata a maganarka.
75
Ya Ubangiji na sani, cewa dokokinka masu adalci ne, kuma cikin aminci ka hore ni.
76
Bari ƙaunarka marar ƙarewa tă yi mini ta’aziyya, bisa ga alkawarinka ga bawanka.
77
Bari tausayinka yă zo mini don in rayu, gama dokarka ce farin cikina.
78
Bari masu girman kai su sha kunya saboda abubuwa marasa kyau da suke yi mini ba dalili; amma zan yi tunani a kan farillanka.
79
Bari waɗanda suke tsoronka su juya gare ni, waɗanda suka gane da farillanka.
80
Bari zuciyata ta kasance marar abin zargi wajen ƙa’idodinka, don kada in sha kunya.
Settings