Zabura 119:65-72
65
Ka yi wa bawanka alheri bisa ga maganarka, ya Ubangiji.
66
Ka koya mini sani da kuma hukunci mai kyau, gama na gaskata a umarnanka.
67
Kafin in sha wahala na kauce, amma yanzu ina biyayya da maganarka.
68
Kai nagari ne, kuma abin da kake yi yana da kyau; ka koya mini ƙa’idodinka.
69
Ko da yake masu fariya sun shafe ni da ƙarairayi, na kiyaye farillanka da dukan zuciyata.
70
Zukatansu sun yi tauri da kuma marasa tausayi amma ina farin ciki a dokarka.
71
Ya yi kyau da na sha wahala don in koyi ƙa’idodinka.
72
Doka daga bakinka ya fi mini daraja fiye da azurfa da zinariya guda dubu.
Settings