Zabura 109:9-15
9
Bari ’ya’yansa su zama marayu matarsa kuma gwauruwa.
10
Bari ’ya’yansa su zama masu yawo suna bara; bari a yi ta koransu daga gidajensu da suke kufai.
11
Bari mai binsa bashi yă ƙwace dukan abin da yake da shi; bari baƙi su washe amfanin aikinsa.
12
Bari kada kowa yă yi masa alheri ko yă ji tausayin marayunsa.
13
Bari duk zuriyarsa su mutu, a shafe sunayensu daga tsara mai zuwa.
14
Bari a tuna da laifin kakanninsa a gaban Ubangiji; bari kada a taɓa shafe zunubin mahaifiyarsa.
15
Bari zunubansu su kasance a gaban Ubangiji kullum, don yă sa a manta da su daga duniya.
Settings