Skip to content
Zabura 109:6-20

Zabura 109:6-20

6
Ka naɗa mugun mutum yă yi hamayya da shi; bari mai zargi yă tsaya a hannun damansa.
7
Sa’ad da aka yi masa shari’a, bari a same shi da laifi, bari kuma addu’o’insa su hukunta shi.
8
Bari kwanakinsa su zama kaɗan; bari wani yă ɗauki wurinsa na shugabanci.
9
Bari ’ya’yansa su zama marayu matarsa kuma gwauruwa.
10
Bari ’ya’yansa su zama masu yawo suna bara; bari a yi ta koransu daga gidajensu da suke kufai.
11
Bari mai binsa bashi yă ƙwace dukan abin da yake da shi; bari baƙi su washe amfanin aikinsa.
12
Bari kada kowa yă yi masa alheri ko yă ji tausayin marayunsa.
13
Bari duk zuriyarsa su mutu, a shafe sunayensu daga tsara mai zuwa.
14
Bari a tuna da laifin kakanninsa a gaban Ubangiji; bari kada a taɓa shafe zunubin mahaifiyarsa.
15
Bari zunubansu su kasance a gaban Ubangiji kullum, don yă sa a manta da su daga duniya.
16
Gama bai taɓa yin tunanin yin alheri ba, amma ya tsananta wa matalauta da mabukata da kuma masu fid da zuciya har suka mutu.
17
Yana jin daɗin la’antarwa, bari yă dawo a kansa; ba ya son sa albarka, bari kada kowa yă sa masa albarka.
18
Ya sa la’antarwa kamar rigarsa; ta shiga cikin jikinsa kamar ruwa, cikin ƙasusuwansa kamar mai.
19
Bari tă zama kamar mayafin da aka ɗaura kewaye da shi, kamar ɗamara da aka ɗaura kewaye da shi har abada.
20
Bari wannan yă zama sakayyar Ubangiji ga masu zargina, ga waɗanda suke mugayen maganganu a kaina.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options