Zabura 109:21-29
21
Amma kai, ya Ubangiji Mai Iko Duka, ka yi da ni da kyau saboda sunanka; ta alherin ƙaunarka, ka cece ni.
22
Gama ni matalauci ne mai bukata kuma, zuciyata kuwa ta yi rauni a cikina.
23
Na ɓace kamar inuwar yamma; ana kakkaɓe ni kamar fāra.
24
Gwiwoyina suna mutuwa saboda azumi; jikina ya rame ba kuma ƙarfi.
25
Na zama abin dariya ga masu zargina; sa’ad da suka gan ni, suka kaɗa kawunansu.
26
Ka taimake ni, ya Ubangiji Allahna; ka cece ni bisa ga ƙaunarka.
27
Bari su san cewa hannunka ne, cewa kai ne, ya Ubangiji, ka yi shi.
28
Za su iya la’anta, amma kai za ka sa albarka; sa’ad da suka tasar za su sha kunya, amma bawanka zai yi farin ciki.
29
Masu zargina za su sha kunya za a rufe su da kunya kamar mayafi.
Settings