Karin Magana 7:11-27
11
(Ba ta jin tsoro, ko kuma kunya, ƙafafunta ba sa zama a gida;
12
wani lokaci a titi, wani lokaci a dandali, tana yawo a kowace kusurwa.)
13
Sai ta kama shi ta rungume shi da duban soyayya a fuskarta ta ce,
14
“Ina da hadaya ta salama a gida; yau zan cika alkawarina.
15
Saboda haka na fito don in sadu da kai; na neme ka na kuma same ka!
16
Na lulluɓe gadona da lili masu launi dabam-dabam daga Masar.
17
Na yayyafa turare a gadona da mur, aloyes da kuma kirfa.
18
Zo, mu sha zurfin ƙauna har safe; bari mu ji wa ranmu daɗi da ƙauna!
19
Mijina ba ya gida; ya yi tafiya mai nisa.
20
Ya ɗauki jakarsa cike da kuɗi ba zai kuwa dawo gida ba sai tsakiyar wata.”
21
Da kalmomin rarrashi ta sa ya kauce; ta ɗauki hankalinsa da sulɓin maganarta.
22
Nan take, ya bi ta kamar saniyar da za a kai mayanka, kamar wawa zuwa wurin da za a ba shi horo
23
sai da kibiya ta soki hantarsa, kamar tsuntsun da ya ruga cikin tarko, ba tare da sani zai zama sanadin ransa ba.
24
Yanzu fa, ’ya’yana, ku saurare ni; ku kasa kunne ga abin da nake faɗa.
25
Kada ku bar zuciyarku ta juya zuwa hanyoyinta ko ku kauce zuwa hanyoyinta.
26
Ta zama sanadin fāɗuwar yawanci; kisan da ta yi ba ta ƙidayuwa.
27
Gidanta babbar hanya ce zuwa kabari mai yin jagora zuwa ɗakunan lahira.
Settings