Karin Magana 30:33
Ana nuna aya 33 tare da mahallin da ke kewaye.
30
zaki mai ƙarfi a cikin namun jeji, wanda ba ya ratse wa kowa;
31
zakara mai taƙama, da bunsuru, da kuma sarki mai sojoji kewaye da shi.
32
“In ka yi wauta ka kuma ɗaukaka kanka, ko kuwa wani yana ƙulla maka mugunta, ka dāfa hannunka a bisa bakinka!
33
Gama kamar yadda kaɗaɗɗen madara takan kawo mai, murɗa hanci kuma takan sa a yi haɓo, haka tsokanar fushi takan kawo faɗa.”
Settings