Karin Magana 19:4-9
4
Wadata kan kawo abokai da yawa, amma abokin matalauci kan bar shi.
5
Mai ba da shaidar ƙarya ba zai tafi babu hukunci ba, kuma duk wanda ya baza ƙarairayi ba zai kuɓuta ba.
6
Kowa na ƙoƙari ya sami farin jini wurin mai mulki, kuma kowa na so a ce shi abokin mutumin nan mai yawan kyauta ne.
7
’Yan’uwan matalauci sukan guje shi, balle abokansa, su ma za su guje shi. Ko da yake matalaucin yana binsu yana roƙo, ba zai sam su ba.
8
Duk wanda ya sami hikima yana ƙaunar ransa; duka wanda yake jin daɗi fahimi kan ci gaba.
9
Mai shaidar ƙarya ba zai tafi babu hukunci ba, kuma duk mai baza ƙarairayi zai hallaka.
Settings