Tabbaci da gaisuwa ta ƙarshe
21
Da tabbacin biyayyarka, ina rubuta maka, da sanin za ka yi fiye da abin da na ce.
22
Abu guda ya rage, ka shirya mini masauƙi, domin ina bege za a mayar da ni gare ku albarkacin addu’o’inku.
23
Efafaras, abokin tarayyata a kurkuku cikin Kiristi Yesu, yana gaishe ka.
24
Haka kuma Markus, Aristarkus, Demas da kuma Luka, abokan aikina.
25
Alherin Ubangiji Yesu Kiristi yă kasance da ruhunku.
Settings