Skip to content
Ƙidaya 6:1-12

Ƙidaya 6:1-12

1
Ubangiji ya ce wa Musa,
2
“Yi magana da Isra’ilawa, ka ce musu, ‘In mace, ko namiji yana so yă yi alkawari na musamman, alkawarin zaman keɓaɓɓe ga Ubangiji, a matsayin Banazare,
3
dole yă keɓe kansa daga ruwan inabi, ko daga waɗansu abubuwa sha masu sa maye, kada kuma yă sha ruwan tsamin da aka yi daga ruwan inabi, ko daga waɗansu abubuwa sha masu sa maye. Ba zai sha ruwan ’ya’yan inabi, ko yă ci ’ya’yan inabi ɗanye ko busasshe ba.
4
Muddin yana Banazare, ba zai ci wani abin da ya fito daga ’ya’yan inabi ba, ko ƙwayar inabi, ko ɓawonsa ma.
5
“ ‘A dukan lokacin da yake a kan alkawarin keɓewarsa, reza ba zai taɓa kansa. Dole yă kasance da tsarki har ƙarshen keɓewarsa ga Ubangiji; tilas yă bar gashin kansa yă yi tsawo.
6
A dukan kwanakin keɓewarsa ga Ubangiji, Banazarin ba zai yi kusa da gawa ba.
7
Ko da ma gawar ta mahaifinsa ce, ko ta mahaifiyarsa, ko ta ɗan mahaifiyarsa, ko kuma ta ’yar’uwarsa ce, ba zai ƙazantar da kansa saboda su ba, domin alamar keɓewarsa ga Allah tana kansa.
8
A dukan kwanakin keɓewarsa, an tsarkake shi ga Ubangiji.
9
“ ‘In farat ɗaya wani ya mutu kusa da shi, to, keɓewarsa ta ƙazantu, dole yă aske kansa a ranar tsarkakewarsa, a rana ta bakwai.
10
Sa’an nan a rana ta takwas, tilas yă kawo wa firist ’yan kurciyoyi biyu, ko kuma ’yan tattabarai biyu a bakin ƙofar Tentin Sujada.
11
Firist kuwa zai miƙa ɗaya don hadaya ta zunubi, ɗayan kuma don hadaya ta ƙonawa, yă yi kafara dominsa, gama ya yi zunubi ta dalilin gawar. A wannan rana zai sāke keɓe kansa.
12
Dole yă keɓe kansa ga Ubangiji, har kwanakin keɓewarsa, kuma dole yă kawo ɗan rago bana ɗaya a matsayin hadayar laifi. Kwanakin baya ba sa cikin lissafi, domin ya ƙazantu a lokacin keɓewarsa.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options