Ƙidaya 6:1-8
1
Ubangiji ya ce wa Musa,
2
“Yi magana da Isra’ilawa, ka ce musu, ‘In mace, ko namiji yana so yă yi alkawari na musamman, alkawarin zaman keɓaɓɓe ga Ubangiji, a matsayin Banazare,
3
dole yă keɓe kansa daga ruwan inabi, ko daga waɗansu abubuwa sha masu sa maye, kada kuma yă sha ruwan tsamin da aka yi daga ruwan inabi, ko daga waɗansu abubuwa sha masu sa maye. Ba zai sha ruwan ’ya’yan inabi, ko yă ci ’ya’yan inabi ɗanye ko busasshe ba.
4
Muddin yana Banazare, ba zai ci wani abin da ya fito daga ’ya’yan inabi ba, ko ƙwayar inabi, ko ɓawonsa ma.
5
“ ‘A dukan lokacin da yake a kan alkawarin keɓewarsa, reza ba zai taɓa kansa. Dole yă kasance da tsarki har ƙarshen keɓewarsa ga Ubangiji; tilas yă bar gashin kansa yă yi tsawo.
6
A dukan kwanakin keɓewarsa ga Ubangiji, Banazarin ba zai yi kusa da gawa ba.
7
Ko da ma gawar ta mahaifinsa ce, ko ta mahaifiyarsa, ko ta ɗan mahaifiyarsa, ko kuma ta ’yar’uwarsa ce, ba zai ƙazantar da kansa saboda su ba, domin alamar keɓewarsa ga Allah tana kansa.
8
A dukan kwanakin keɓewarsa, an tsarkake shi ga Ubangiji.
Settings