Ƙidaya 19:11-16
11
“Duk wanda ya taɓa gawa, zai kasance da ƙazanta har kwana bakwai.
12
Dole yă tsarkake kansa da ruwa a rana ta uku, da kuma a rana ta bakwai; sa’an nan zai zama da tsarki. Amma in bai tsarkake kansa a rana ta uku da kuma a rana ta bakwai ba, ba zai kasance da tsarki ba.
13
Duk wanda ya taɓa gawar wani, bai kuma tsarkake kansa ba, ya ƙazantar da tabanakul na Ubangiji ke nan. Dole a ware wannan mutum daga cikin Isra’ilawa. Gama ba a yayyafa ruwan tsabtaccewa a kansa ba; ya ƙazantu, ya kasance da ƙazanta ke nan.
14
“Ga ƙa’idar da za a bi in mutum ya mutu a cikin tenti. Duk wanda ya shiga tentin, kuma duk wanda yake cikinsa, za su zama da ƙazanta har kwana bakwai,
15
kuma kowane abin da ake zuba kaya, wanda ba shi da murfi a kansa, zai zama da ƙazanta.
16
“Wanda duk yake a fili, ya kuma taɓa gawa wanda aka kashe da takobi, ko wanda ya mutu mutuwar Allah, ko ƙashin mutum, ko kabari, zai ƙazantu har bakwai.
Settings