Skip to content
Ƙidaya 19:1-10

Ƙidaya 19:1-10

1
Ubangiji ya ce wa Musa da Haruna,
2
“Wannan ita ce ƙa’ida wadda Ubangiji ya umarta. Faɗa wa Isra’ilawa su kawo maka jan karsana marar lahani, ko marar aibi wadda ba a taɓa sa ta tă yi noma ba.
3
Ka ba wa Eleyazar firist; a kuma kai ta bayan sansani, a yanka a gaban Eleyazar.
4
Sa’an nan Eleyazar firist zai ɗiba jininta a yatsarsa, yă yayyafa sau bakwai wajen gaban Tentin Sujada.
5
Sa’an nan a ƙone dukan karsanar, haɗe da fatarta, naman, jinin da kayan cikin, yayinda Eleyazar yake kallo.
6
Firist zai ɗauki itacen al’ul, da hizzob, da jan ulu, yă jefa su a kan karsanar da ake ƙonewa.
7
Bayan haka, dole firist yă wanke rigunarsa, yă kuma yi wanka. Sa’an nan zai iya shiga cikin sansani, amma zai kasance da ƙazanta har yamma.
8
Dole mutumin da ya ƙone ta yă wanke rigunarsa, yă kuma yi wanka, shi ma zai kasance da ƙazanta har yamma.
9
“Mutumin da yake da tsarki, zai tara tokar karsanar, yă sa ta a wurin da yake da tsabta a bayan sansani. Jama’ar Isra’ilawa ne za su adana shi don amfani a ruwan tsabtaccewa; wannan domin tsarkakewa ne daga zunubi.
10
Dole mutumin da ya tara tokar karsanar yă wanke rigunarsa, zai kuwa kasance da ƙazanta har yamma. Wannan za tă zama dawwammamiyar farilla ta har abada ga Isra’ilawa, da kuma baƙin da suke zama a cikinsu.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options