Skip to content
Ƙidaya 18:8-20

Ƙidaya 18:8-20

8
Sai Ubangiji ya ce wa Haruna, “Na ba ka aikin lura da hadayun da za a miƙa mini, dukan tsarkakan hadayun da Isra’ilawa suka ba ni, na ba ka su su zama rabonka da na ’ya’yanka har abada.
9
Kai za ka riƙe sashe mafi tsarki na hadayun da suka ragu daga wuta. Daga dukan kyautai mafi tsarki na hadayun da suka miƙa mini, ko ta gari, ko don zunubi, ko kuma don laifi, wannan kashi naka ne da ’ya’yanka.
10
Ku ci shi a matsayin abu mafi tsarki; kowane namiji zai ci. Dole ku ɗauke shi da tsarki.
11
“Har yanzu kuma duk abin da aka keɓe daga kyautai na dukan hadayun kaɗawa na Isra’ilawa naka ne. Na ba da wannan gare ka da ’ya’yanka maza da mata, a kowane lokaci. Kowa da yake da tsarki a gidanka zai iya ci.
12
“Na ba ka duk man zaitun mafi kyau, da ruwan inabi mafi kyau duka, da hatsi mafi kyau duka na nunan farinsu da suke bayarwa ga Ubangiji.
13
Dukan nunan fari na ƙasar da suke kawo wa Ubangiji, zai zama naka. Kowa da yake da tsarki a gidanka zai iya ci.
14
“Kome a Isra’ila da aka keɓe wa Ubangiji, zai zama naka.
15
Kowane haihuwar fari, ta mutum, ko ta dabba da suka miƙa wa Ubangiji, naka ne. Amma ka fanshi kowace haihuwar fari ta mutum, ko ta dabbar da take haram.
16
Sa’ad da suke wata ɗaya da haihuwa, dole a fanshe su a bakin shekel biyar-biyar, bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri da ake amfani da shi, wanda nauyinsa ya kai gera ashirin.
17
“Amma kada ka fanshe ɗan fari na saniya, tunkiya, ko akuya; gama suna da tsarki. Ka yayyafa jininsu a bisan bagade, ka kuma ƙone kitsensu kamar hadayar da ka yi da wuta, mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji.
18
Namansu zai zama naka, haka ma ƙirji na kaɗawa da cinyar dama za su zama naka.
19
Kome da aka keɓe daga tsarkakakku hadayun da Isra’ilawa suka miƙa wa Ubangiji, na ba ka, da kai da ’ya’yanka maza da mata a matsayin zaunannen rabo. Wannan madawwamin alkawarin gishiri ne a gaban Ubangiji dominka da zuriyarka.”
20
Ubangiji ya ce wa Haruna, “Ba ka da gādo a ƙasarsu, ba kuwa za ka sami rabo daga cikinsu ba; ni ne rabonka da gādonka a cikin Isra’ilawa.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options