Ƙidaya 15:1-15
1
Ubangiji ya ce wa Musa,
2
“Ka yi magana da Isra’ilawa, ka ce musu, ‘Bayan kun shiga ƙasar da nake ba ku a matsayin gida,
3
kuka yi hadayar da akan yi da wuta ga Ubangiji, daga cikin shanu, ko tumaki, abin ƙanshi mai daɗi ga Ubangiji, ko hadaya ta ƙonawa, ko hadayu don alkawura na musamman, ko hadayar yardar rai, ko kuma hadaya ta biki,
4
sai shi wanda ya kawo hadayar yă miƙa wa Ubangiji hadaya ta gari mai laushi mai kyau, kashi ɗaya bisa goma na efa wanda aka kwaɓa da kwalaba ɗaya na mai.
5
Da kowane ɗan rago don hadaya ta ƙonawa, a shirya kwalaba ɗaya na ruwan inabi, a matsayin hadaya ta sha.
6
“ ‘In da rago ne za a miƙa, to, sai a shirya hadaya ta gari mai laushi, garin yă zama kashi biyu bisa goma na efa. A kwaɓa shi da kashi ɗaya bisa uku na garwan mai,
7
da kashi ɗaya bisa uku na garwan ruwan inabi, a matsayin hadaya ta sha. A miƙa ta abin ƙanshi mai daɗi ga Ubangiji.
8
“ ‘Sa’ad da kuka shirya rago don hadaya ta ƙonawa saboda alkawari na musamman, ko hadaya ta salama ga Ubangiji,
9
sai ku kawo hadaya ta gari tare da bijimi, kashi ɗaya bisa uku na gari mai laushi kwaɓaɓɓe da rabin garwan mai.
10
A kuma kawo rabin garwan ruwan inabi na hadaya ta sha. Za tă zama hadayar da aka yi da wuta mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji.
11
Haka za a yi da kowane bijimi, ko rago, ko ɗan rago, ko bunsuru.
12
Haka za a yi da kowannensu bisa ga abin da aka shirya.
13
“ ‘Duk wanda yake ɗan ƙasa, ta haka ne dole zai aikata waɗannan abubuwa sa’ad da ya kawo hadaya da akan yi da wuta mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji.
14
Idan baƙon da yake baƙunci a cikinku, ko kowane ne da yake tare da ku a dukan zamananku, yana so yă ba da hadayar da akan yi da wuta don a yi ƙanshi mai daɗi ga Ubangiji, dole yă yi kamar yadda kuke yi.
15
Ƙa’ida ɗaya ce ga jama’a da kuma baƙin da suke zama a cikinku, wannan za tă zama dawwammamiyar farilla a dukan tsararraki masu zuwa. Da ku, da baƙi, za ku zama ɗaya a gaban Ubangiji.
Settings