Skip to content
Nehemiya 11:1-4

Nehemiya 11:1-4

1
To, fa, shugabannin mutane suka zauna a Urushalima, sauran mutanen kuma suka jefa ƙuri’a don su kawo mutum ɗaya daga kowane mutum goma don su zauna a Urushalima, birni mai tsarki, yayinda sauran tara suka zauna a garuruwansu.
2
Sai mutane suka yaba wa dukan mutanen da suka ba da kansu da yardar rai su zauna a Urushalima.
3
Waɗannan su ne shugabannin yankuna waɗanda suka zauna a Urushalima (ko da yake waɗansu Isra’ilawa, da firistoci, da Lawiyawa, da ma’aikatan haikali, da zuriyar bayin Solomon, suka yi zama a cikin garuruwan Yahuda, kowanne a mallakarsa cikin garuruwa dabam-dabam,
4
yayinda sauran mutane daga Yahuda da Benyamin suka zauna a Urushalima). Daga zuriyar Yahuda akwai, Atahiya ɗan Uzziya, ɗan Zakariya, ɗan Amariya, ɗan Shefatiya, ɗan Mahalalel, wani zuriyar Ferez;
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options