Nehemiya 10:32-39
32
“Mun ɗauka hakkin bin umarnai na ba da kashi ɗaya bisa uku na shekel kowace shekara don hidimar gidan Allahnmu.
33
Za mu tanada burodin da ake ajiye a kan tebur; za mu ba da hadayun hatsi da hadayun ƙonawa na kullum; za mu ba da hadayun Asabbatai, da na bukukkuwan Sabon Wata da na bukukkuwan da aka ƙayyade; za mu ba da hadayu masu tsarki; za mu ba da hadayun zunubi don a yi kafara domin Isra’ila; mu kuma ba da abubuwan da ake bukata dukan domin ayyukan gidan Allahnmu.
34
“Mu, firistoci, da Lawiyawa da kuma mutane, mun jefa ƙuri’a don a san lokacin da kowane iyalinmu zai kawo sadakar itace don ƙonewa a gidan Allahnmu a ƙayyadaddun lokuta a bagaden Ubangiji Allahnmu, kamar yadda yake a rubuce a cikin Doka.
35
“Mun kuma ɗauka hakkin kawo nunan fari na hatsinmu da kuma na kowane itace mai ba da ’ya’ya a gidan Ubangiji kowace shekara.
36
“Kamar yadda yake a rubuce a cikin Doka, za mu kawo ɗan fari na ’ya’yanmu maza da na garken shanunmu, da na tumakinmu, da kuma na awakinmu a gidan Allahnmu, don firistocin da suke aikin a can.
37
“Ban da haka ma, za mu kawo wa ɗakunan ajiyar gidan Allahnmu, abincinmu na farko daga ƙasa, na hadayun hatsinmu, na ’ya’yan dukan itatuwanmu da kuma na sabon ruwan inabinmu da mai namu wa firistoci. Za mu kuma kawo zakkar hatsinmu wa Lawiyawa, gama Lawiyawa ne ke karɓan Zakka cikin dukan garuruwan da muke noma.
38
Firist wanda yake daga zuriyar Haruna zai raka Lawiyawa sa’ad da suke karɓan zakka, Lawiyawan kuma za su kawo kashi ɗaya bisa goma na zakka zuwa gidan Allahnmu, su kawo a ɗakunan ajiya na baitulmali.
39
Mutanen Isra’ila haɗe da Lawiyawa, za su kawo sadakokinsu na hatsi, sabon ruwan inabi da mai a ɗakunan ajiya inda ake ajiyar kayayyakin wuri mai tsarki da kuma inda firistoci, matsaran ƙofofi da kuma mawaƙa suke zama. “Ba za mu ƙyale gidan Allahnmu ba.”
Settings