Skip to content
Nahum 1:2-8

Nahum 1:2-8

2
Ubangiji Allah mai kishi ne, mai sakayya kuma. Ubangiji Allah mai kishi ne, mai ɗaukar fansa kuma. Ubangiji yakan ɗauki fansa a kan maƙiyansa, yakan ci gaba da fushi a kan abokan gābansa.
3
Ubangiji mai jinkirin fushi ne, mai iko duka kuma. Ubangiji ba zai bar masu zunubi babu horo ba. Hanyarsa tana cikin guguwa da kuma hadari, gizagizai kuwa su ne ƙurar ƙafafunsa.
4
Yakan tsawata wa teku yă kuma busar da shi; yakan sa dukan koguna su kafe. Bashan da Karmel sun yi yaushi tohon Lebanon kuma ya koɗe.
5
Duwatsu suna rawan jiki a gabansa tuddai kuma sun narke. Duniya da dukan abin da yake cikinta suna rawan jiki a gabansa.
6
Wa zai iya tsaya wa fushinsa? Wa yake da ikon jimre wa zafin hasalarsa? Ana zuba fushinsa kamar wuta; aka kuma ragargaza duwatsu a gabansa.
7
Ubangiji nagari ne, mafaka kuma a lokacin wahala. Yana kula da waɗanda suka dogara gare shi,
8
amma da ambaliyar ruwa zai kawo Ninebe ga ƙarshe; zai fafari maƙiyansa zuwa cikin duhu.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options