Mika 7:7-10
7
Amma game da ni, zan sa bege ga Ubangiji, ina sauraron Allah Mai Cetona; Allahna kuwa zai ji ni.
8
Kada ku yi farin ciki, ku maƙiyana! Ko da yake na fāɗi, zan tashi. Ko da yake na zauna a cikin duhu, Ubangiji zai zama haskena.
9
Domin na yi masa zunubi, zan fuskanci fushin Ubangiji, har sai ya dubi batuna ya kuma tabbatar da ’yancina. Zai kawo ni zuwa wurin haske; zan ga adalcinsa.
10
Sa’an nan maƙiyina zai gani yă kuma sha kunya, shi da yake ce da ni “Ina Ubangiji Allahnka?” Zai gani, yă kuma ji kunya. Ko yanzu ma za a tattake shi kamar taɓo a tituna.
Settings