Skip to content
Mika 7:1-6

Mika 7:1-6

1
Tawa ta ƙare! Ina kama da wanda yake tattara ’ya’yan itatuwa a lokacin kalar ’ya’yan inabi; babu sauran nonon inabin da za a tsinka a ci, babu kuma ’ya’yan ɓaure na farko-farkon da raina yake marmari.
2
An kawar da masu tsoron Allah daga ƙasar; babu sauran mai adalcin da ya rage. Dukan mutane suna kwanto don su zub da jini; kowa yana farautar ɗan’uwansa da tarko.
3
Dukan hannuwansu sun gwaninta wajen yin mugunta; shugabanni suna nema a ba su kyautai, alƙalai suna nema a ba su cin hanci, masu iko suna faɗar son zuciyarsu, duk suna ƙulla makirci tare.
4
Mafi kyau a cikinsu yana kama da ƙaya, mafi gaskiyarsu ya fi shingen ƙaya muni. Ranar da Allah zai ziyarce ku ta zo, ranar da masu gadinku za su hura ƙaho. Yanzu ne lokacin ruɗewarku.
5
Kada ka yarda da maƙwabci; kada ka sa begenka ga abokai. Ko ma wadda take kwance a ƙirjinka, ka yi hankali da kalmominka.
6
Gama ɗa yakan ce wannan ba mahaifinsa ba ne, diya kuma takan tayar wa mahaifiyarta, matar ɗa takan yi gāba da uwar mijinta, abokan gāban mutum su ne iyalin cikin gidansa.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options