Mattiyu 9:20
Ana nuna aya 20 tare da mahallin da ke kewaye.
17
Mutane kuma ba sa zuba sabon ruwan inabi a cikin tsofaffin salkuna. In suka yi haka, salkunan za su farfashe, ruwan inabin kuwa yă zube salkunan kuma su lalace. A’a, ai, sukan zuba sabon ruwan inabi ne a cikin sababbin salkuna, don a kiyaye dukan biyun.”
18
Yayinda yake faɗin wannan, sai wani mai mulki ya zo ya durƙusa a gabansa ya ce, “Yanzu-yanzu diyata ta rasu. Amma ka zo ka ɗibiya hannunka a kanta, za tă kuwa rayu.”
19
Yesu ya tashi ya tafi tare da shi, haka ma almajiransa.
20
A daidai wannan lokaci sai ga wata mace wadda ta yi shekaru goma sha biyu tana zub da jini ta raɓo ta bayansa ta taɓa gefen rigarsa.
21
Ta ce a ranta, “Ko da rigarsa ce kawai na taɓo, zan warke.”
22
Yesu ya juya ya gan ta. Sai ya ce, “Kada ki damu diyata, bangaskiyarki ta warkar da ke.” Nan take macen ta warke.
23
Da Yesu ya shiga gidan mai mulkin ya ga masu busan sarewa da taro mai hayaniya,
Settings