Skip to content
Mattiyu 24:29-31

Mattiyu 24:29-31

29
“Nan da nan bayan tsabar wahalan nan “ ‘sai a duhunta rana, wata kuma ba zai ba da haskensa ba; taurari kuma za su fāffāɗi daga sararin sama, za a kuma girgiza abubuwan sararin sama.’
30
“A sa’an nan ne alamar dawowar Ɗan Mutum zai bayyana a sararin sama, dukan al’umman duniya kuwa za su yi kuka. Za su ga Ɗan Mutum yana zuwa kan gizagizan sararin sama, da iko da kuma ɗaukaka mai girma.
31
Zai kuwa aiki mala’ikunsa su busa ƙaho mai ƙara sosai, za su kuwa tattaro zaɓaɓɓunsa daga kusurwoyi huɗun nan, daga wannan bangon duniya zuwa wancan.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options